20 Maris 2026 - 16:46
Source: ABNA24
Iran: Mai Gana Da Yawun Irgc Sayyid Naeini Yayi Shahada

Babbar Cibiyar hafsan soji da sansanin Hazrat Khatamal Anbia (SAW) a sakon ta’aziyarta ga shahadar kwamanda Naeini ta tabbatar da cewa: Shahidin Mujahidi Ali Muhammad Naeini Ya sadaukar da kansa ga jihadi don Allah fiye da shekaru arba'in na rayuwarsa, kuma a safiyar ranar karshen watan Ramadan mai alfarma, ya cimma burinsa na dogon lokaci a harin masu aikata laifukan ta'addanci na Amurka Isra’ila.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA): Babbar cibiyar hafsoshin soji da babbar cibiyar Hazrat Khatamul-Anbiya (SAW) sun jaddada a cikin wannan sakon: Shahada fasahar ala’ada ce ta mutanen Allah. Madaukakin Shahidi mai babban matsayi shahid Naeini ya kasance a matsayin tunani, nazari, aiki, alkalami da magana, takobi mai kaifi a cikin zukatan makiya juyin juya halin Musulunci ya kasance kamar ƙaya a idanunsu. Ya kamata mugayen makiyan kasa da al’umma su san cewa ta hanyar kashe masu ruwayar fagen gaskiya da ke fuskantar fagen shaidan, ba za su iya rufe muryar gaskiya ba.

Sakon Babbar cibiyar Hafsoshin Sojoji na Shahadar Sardar Naeini shi ne kamar haka:

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Kai.

بسم الله الرحمن الرحیم

وَلَا تَحْسَبَنَّ الَّذِینَ قُتِلُوا فِی سَبِیلِ اللَّهِ أَمْوَاتًا بَلْ أَحْیَاءٌ عِنْدَ رَبِّهِمْ یُرْزَقُونَ

Kuma babban tushe na Hazrat Khatam al-Anbiya (SAW): Shahada fasaha ce ta mutanen Allah. Shahadar Mujahid Nastooh kwamandan da baya gajiya a fagen al’adu da yaki, madaukakin shahidi Birgediya Janar Ali Muhammad Naeini, mataimakin hukumar hulda da jama'a kuma mai magana da yawun dakarun kare juyin juya halin Musulunci na mika sakon ta’ziyya da murna ga Hazrat Waliyil-Asr (Af) ga kuma Babban Kwamandan (Maddazilleihul-Aali) ga dakarun juyin juya halin musulunci ga kuma dakarun Basij, ga kuma daidaikun dakarun gwagwgarmayar Musulunci, ga kuma iyalan wannan shahidi mai girma, ga kuma musamman ma ma’aikata kafafen yada labarai. Mujahid Shahidin Mujahidi Ali Muhammad Naeini Ya sadaukar da kansa ga jihadi don Allah fiye da shekaru arba'in na rayuwarsa, kuma a safiyar ranar karshen watan Ramadan mai alfarma, ya cimma burinsa na dogon lokaci a harin masu aikata laifukan ta'addanci na Amurka Isra’ila.

Madaukakin Shahidi mai babban matsayi shahid Naeini ya kasance a matsayin tunani, nazari, aiki, alkalami da magana, takobi mai kaifi a cikin zukatan makiya juyin juya halin Musulunci ya kasance kamar ƙaya a idanunsu. Ya kamata mugayen makiyan kasa da al’umma su san cewa ta hanyar kashe masu ruwayar fagen gaskiya da ke fuskantar fagen shaidan, ba za su iya rufe muryar gaskiya ba. Kuma rashin nasara fagen shaidan daya bayan day aba zai boyu b aga idanun al’ummar duniya ba.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha